Sabon Fim Din Tarko Na Tafe Don Matafiya Kasashen Waje

Tijjani Shehu Yahaya

Tijjani Shehu Yahaya – ya bayyana cewar a yanzu yana aiki ne akan wata dabi’a da ke ci masa tuwo a kwarya, wato yadda matasa sai sun cimma wani buri na yin arziki ta hanyar tafiya kasashen ketare, ba tare da suna da cikakkun takardun da suka dace ba wato ta haramtaciyyar hanya.

A ta bakin furudusa Tijjani, abinda ya ja hankalin shi wajen shirya wannan fim na neman arziki ta hanyar gudun hijira ta hanyar da bata dace ba, duba da yadda wadannan matasan ke mutuwa a hanya kafin su kai ga kasashen da suka sa a gaba, ganin ire-iren wahalhalun da suka sha a kasashe kamar su Saudia, Algeria da Jamus da ma kasar Italy.

Ya kara da cewa a baya bayan nan ne wasu kasashen suka rika dawo da mutanen da suka shiga kasashen su, ta haramtaciyar hanya, wasu tare da iyayensu suke tafiya, wasu kuma sun jima da barin garuruwansu dan haka mayar da su kasar su ta asali ya zame musu tamkar suna bakuwar kasa, saboda basu san daga inda zasu fara neman 'yan uwansu ba.

Tijjani ya ce za’a fara fim dinne daga kasashen Faransa, Algeria da kuma Jamus, inda ya ce tuni aka yi nisa da rubuta fim din kuma fim din zai kasance da yarukan wadannan kasashe da suke shiga domin neman arziki.

Daga karshe Malam Tijjani, ya ce yana fata idan fim din ya fito ya zama kamar wata izna ta daukewa matasa hankali ga fita neman arziki tare da nuna masu irin hadurran da ke tattare da yin hakan.