Yau Lahadi sabon babban sakataren MDD Antonio Guterres zai karbi shugabancin hukumar ta duniya, bayan da wa'adin magatakardan MDD mai barin gado Ban ki-moon ya kare da karfe 12 na dare jiya Asabar 31 ga watan Disemba.
Guterres, wanda tsohon PM Portugal ne, kuma tsohon kwamishinan hukumar kula da 'yan gudun hijira na MDD, a cikin jawabi d ya gabatar ya gayawa MDD cewa batun yadda za'a taimakawa miliyoyin mutane wadanda yake yake suka rutsa da su ko suka zasu a tsakiya, shine babban baunda yake ta tunani akai.
Ya lura cewa farar hula suna fuskantar kazamin farmaki, ana kashe su a jikkata su,a tilasta musu barin muhallansu,a jefa su cikin talauci. Ya bayyaan damuwar ganin koda asibitoci da kungiyoyin agaji basu tsira daga tarzomar ba.
Guterres, yayi kira ga takwarorinsa jakadu a MDD "su yi alkawari ko kuduri a sabuar shekaran nan cewa "zasu fifita aiki na samun zaman lafiya gaba da komi."
Ahalinda ake ciki kuma, kwamitin sulhu na MDD baki dayansa ya amince da shirin tsagaita a rikicin da ake yi a Syria, wanda kasashen Rasha da Turkiyya suka shiga tsakani aka kulla, duk da haka rahotanni daga fagen daga suna cewa yarjejeniyar wacce tayi kwanaki biyu tana aiki tana fuskantar barazanar wargajewa.