Kungiyar mayakan sakai ta al-Shabab a Somalia ta zartas da hukuncin kisa kan uku daga cikin ‘yan kungiyar, bisa zargin suna yi wa kungiyoyin leken asirin Amurka, da Britaniya leken asiri.
Wani dandalin a yanar internet dake goyon bayan al-shabab, yace ranar lahadi ne aka kashe mutanen a garin Merka.
Wani alkalin kungiyar yace daya daga cikin mutanen da aka kashen mai suna Mukhtar Ibrahim Sheikh Ahmed, ya amince yana yi wa kungiyar leken asiri ta Ingila M16 leken asiri, da kuma mika wasu musulmi ga hukumomin yankin Somaliland da ya balle.
Alkalin ya ci gaba da cewa mutum na uku Yasin Osman Ahmed da Ishaq Omar Hassan, su kuma an same su da laifin makala na’urori cikin motoci da suka taimakawa jiragen yakin Amurka da basu da matuka, iya bi domin su kai hari kan ‘yan kasashen ketare da suke aiki da kungiyar ta al-Shabab.
A farkon wan nan shekarar ce Amurka tayi amfani da jiragen yakin nan da basu da matuka suka kai hari kan wani dan kasar Lebanon Bilal Al-Barjawi, da kuma wani dan kasar Morocco, Sheikh Abu Ibrahim. An kai harin da ya kashe su ne kusa da birnin Mugadishu.