Sabbin Alkaluman COVID-19 a Najeriya

Farfesa Christian Happi Shugaban Wata Cibiyar Bincike a Najeriya

Gaba dayan adadin wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar COVID-19 a Najeriya ya kai 43,151 a ranar Juma’a 31 ga watan Yuli, a cewar hukumar NCDC da ke sa ido kan cututtuka masu yaduwa.

A bayannan da ta ke fiddawa a kowacce rana a shafinta na Twitter, hukumar ta NCDC ta ce an samu karin mutum 462 da suka kamu da cutar a ranar.

A cewar hukumar, cikin mutum 43,151 da suka kamu da cutar, mutum 19,565 sun warke kuma an sallame su daga asibiti yayin da mutum 879 suka mutu.

Hukumar ta kuma ce an samu karin adadin ne daga jihohi 16 ciki har da birnin tarayya Abuja inda aka samu mutum 93 daga nan sai jihar Lagos inda aka samu mutum 78, 64 a Plateau, 54 a Kaduna.

Sauran jihohin sun hada da Oyo-47, Ondo-32, Adamawa-23, Bauchi-19, Rivers-9, Ogun-9, Delta-9, Edo-7, Kano-6, Enugu-6, Nasarawa-5, Osun-1.