A kalla mutane 40 ne suka mutu sakamakon rushewar madatsar ruwa a kasar Kenya ranar Laraba bayan anyi ruwan sama kamar da bakin kwarya.
Wannan ruwan ya share gidaje da dama da gonaki tare da tsayar da harkokin kasuwanci bayan Dam din dake Solai kilomita 180 a arewa maso yammacin Nairobi yayi ambaliya.
Ian Ndegwa wanda yaga yadda lamarin ya faru ya fada wa sashen Swahili na Muryar Amurka cewa adadin rayukan da suka salwanta na iya zarta abinda aka bada rahoto akai.
Domin akwai mutane da dama da har yanzu ba’a san inda suke ba. Yace akwai ‘yan sanda da sojoji dama magina suna wannan wurin domin ganin sun kwashe abubuwan da suka toshe hanya tare da neman mutanen da suka bata.
Gwamnatin kasar Kenya ta fada a ranar Laraba cewa sakamakon wannan ruwan saman yayi dalilin raba mutane da yawan su ya kai dubu 220 da muhallan su.