Rushewar Gidaje: An Bukaci Legas, Oyo Su Biya Diyya

Jami'an gwamnati a lokacin da suke bincike kan ginin da ya rushe a Legas, Najeriya. Ranar 14 ga watan Maris, 2019.

Kungiyar SERAP mai hankoron ganin an tabbatar da adalci a tsakanin al’umar a Njeriya ta yi kira ga gwamnatocin jihohin Legas da Oyo, da su dauki matakan gaggawa domin ganin an daina take hakkin bil Adama.

Kungiyar ta SERAP, ta yi wannan kira ne a wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Twitter inda ta nemi jihohin da su biya diyya ga iyalan da rushewar gidaje suka shafa a jihohin.

“Ya kamata gwamnan jihar Legas, Akinwumi Ambode da takwaran aikinsa na Oyo, Abiola Ajimobi, su dauki matakan gaggawa wajen tabbatar da cewa an yi wa iyalai adalci, an biya su diyya.”

Sanarwa ta kuma nemi gwamnatocin da su tabbatar cewa, irin wadannan hadurra ba su sake aukuwa ba.

A makon da ya gabata wani bene mai hawa uku ya rushe a jihar Legas inda ya halaka mutum akalla 20 ciki har da daliban firaimari da makarantarsu ke bene na uku.

Har ila yau a cikin makon da ya gabata, wani gini shi ma ya rushe a birnin Ibadan na jihar Oyo da ba ta da nisa daga jihar ta Legas.

Rushewar gidaje ba sabon abu ba ne a Najeriya, musamman a jihar ta Legas da ke kudu maso yammacin kasar.