'Yansandan sun zargi Bashir Dauda da wallafa wani labarin da suka ce ba na gaskiya ba ne a sashen sadarwa ta internet.
To saidai gwamnatin jihar ta fito ta tsame kanta daga kamun da 'yansandan suka yiwa Bashir Dauda, amma tace matashin ya wallafa labarin karya ne.
Mansur Al-Mashi mai baiwa gwamnan jihar shawara akan sha'anin watsa labarai yace gwamnatin jihar bata kai koke wurin 'yansanda ba kuma bata bada umurnin a kama kowa ba.
Al-Mashi yace kowa nada 'yancin fadin albarkacin bakinsa amma wannan ba dama ba ce ta fadin karya musamman abun da ka iya tada hankulan mutane har ya kaiga tashin hankali. Irin hakan na iya kawo salwantar rayuwar mutane tare da dukiyoyinsu.
Ya cigaba da cewa labarin da suka rubuta ya jawo dumamar zaman lafiya a cikin jihar.
A nata bangaren rundunar 'yansandan ta tabbatar da kama sakataren Muryar Talaka na kasa tare da wasu mutane ukku inda tace tuni ta gurfanar dasu a gaban kotu. DSP Salisu Agaisa kakakin rundunar 'yansandan yace 'yancin fadin albarkacin baki bai sa a wuce gona da iri ba.
Mutanen wai sun buga labarin cewa gwamnan jihar Aminu Masari ya sayi makara dubu ukku akan Nera dubu tamanin tamanin da dubu arba'in arba'in an rarrabawa masallatai. Bashir Dauda yayi sharhi akan batun inda yace wai gwamnan yana fatan 'yan jihar su dinga mutuwa ke nan.
Inji DSP Salisu Agaisa mutanen sun amsa laifin da suka yi.
Tuni kungiyar Muryar Talaka tayi watsi da kamun da aka yiwa sakatarenta lamarin da ta kira koma baya ga tsarin dimokradiya da 'yancin bayyana ra'ayi.
Ga rahoton Murtala Faruk da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5