Yace idan mutum ya yi anfani da hannusa ya kai ramuwa to irin hakan shi ya kan kaiga fadace fadace da basa karewa.
Taron da rundunar 'yansandan jihar ta shirya tayi ne domin kawo fahimmtar juna tsakanin makiyaya da manoma da zummar kawo zaman lafiya a jihar.
Rikicin makiyaya da manoma ya kan jawo hasarar rayuka da kuma dimbin dukiyoyi lamarin da ya sa hukumomin tsaro sun tashi tsaye domin kawo karshen tashin tashina..
Mahalarta taron kamar Alhaji Usman Liman Dimsa jigon kungiyar Fulani makiyaya ta Miyetti Allah ya yaba da matakin da rundunar 'yansandan jihar ta dauka.Ya kuma bada shawarar cewa a wannan karon a yi anfani da shawarwarin da suka bayar ba kaman can baya ba da akan yi watsi da abubuwan da suka fada.
Ya cigaba da kiran gwamnatocin kananan hukumomi da na jiha da na tarayya su hadu da sarakunan gargajiya domin a gudanar da adalci. A cire son kai ko banbanci ko kuma bangaranci da kabilanco. Kowa a bashi hakinsa.
Su ma manoma sun ce ashirye suke su bada hadin kai domin kwalliya ta biya kudin sabulu. Mr. Jonathan Mba daya daga cikin shugabannin kungiyar manoma ta jihar ya bada shawarar hanyoyin da ya kamata a bi domin samun zaman lafiya mai dorewa.
Yace babbar matsalar ita ce rashin burtali. Burtalin da manoma sun nome saboda haka babu inda shanu zasu bi su wuce. Ya kira mahukunta su sake duba lamarin.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5