Biyo bayan arangamar da dalibai suka yi da 'yansandan kasar Nijar da ya haddasa mutuwar dalibi daya, wani faifan bidiyo yana ta zagaya kasar wanda yake nuna yadda wasu 'yansanda suka dinga lakadawa dalibin kashi har rai yayi halinsa.
Faifan bidiyon ya ba rundunar 'yansandan kasar Nijar damar gudanar da bincike har sai da ta gano 'yansandan da suka aikata ta'asar, inji kakakin hukumar 'yansandan, Mainasara Adili Toro, yayin da ya kira taron manema labarai.
Yana mai cewa aikin asha ne kuma bai kamata ba. Yace abun da suka yi baya cikin kaidar ayyukan 'yansandan Nijar. Yace dalibin na cikin mota aka hango 'yansandan na bugushi abun da yace bai makata ba. Yace sun nemo 'yansandan cikin gaggawa kuma sun samesu. Yace yanzu ana tsare dasu.
A cewar kakakin 'yansandan su uku ne. Suna hannun masu bincike ta hukumar 'yansandan. Su ne kuma zasu yanke shawara kan yadda za'a yi da mutanen uku. Kafin a kaiga sanin abun da za'a yi dasu sai an kammala bincike akan irin halin da dalibin ya rasu.
Rasuwar dalibin ta haddasa ja-in-ja tsakanin kungiyar dalibai da hukumomin kasar Nijar. Yayinda gwamnati ke cewa dalibin ya fado ne daga bene su kuwa daliban suna zargin 'yansanda da harbe dalibin a ka da barkonon tsohuwa lamarin da ya sa likitoci suka bukaci yin bincike domin tantance dalilin rasuwarsa.
Ga rahoton Souley Barma da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5