Babban sifeton 'yan sandan Najeriya ya ce rundunarsa ta soma gina wata cibiyar bincike a Maiduguri da zata sa ido kan yadda ake kera bama-bamai da wadanda suka kera su da irin abubuwan da suka hada bamabaman dasu.
Babban sifeton 'Yansandan ya bayyana hakan ne lokacin da yake ganawa da manema labarai a garin Maiduguri, lokacin da ya ziyarci cibiyar da yanzu haka ake aikin ginata.A cewarsa nan ba da jimawa ba za'a kammala gina cibiyar wadda za ta zama tamkar makarantar koyas da jami'an yan sandan na musamman da zasu gudanar da ayyukan
Shugaban 'yan sandan ya ce ya sani wasu 'yan sandan ba'a biyasu, yace dalilin haka shine rashin sa hannu a kasafin kudin bana. Yana fatan za'a warware matsalar. Kazalika rundunar ta samar da karnuka na musamman da zasu dinga aiki a yankin da ake kira Munagare da kewayen Jami'ar Maiduguri, inda ake samun yawan kai hare hare. Za'a sa jami'ai na musamman da za su dinga sa ido akan abubuwan dake gudana.
Wadanda aka koyar a cibiyar su ne zasu tantance bam da ya fashe su san inda aka kerashi da irin sinadiran da aka yi anfani dashi.
Babban sifeton ya ziyarci ofishin Gwamnan jihar inda ya ga mataimakin gwamnan jihar kana ya ziyaeci fadar Shehun Borno.
Ga rahoton Haruna Dauda da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5