Rundunar 'Yan Sanda Najeriya Ta Yi Barazanar Ayyana Dino Melaye A Zaman Wanda Take Nema Ruwa A Jallo.

Shugaban Kakakin Majalisar Dattawan Najeriya Bukola Saraki

Sanata Dino Melaye ya shiga takunsaka da rundunar 'yan sanda Najeriya da ta yi barazanar ayyana nemansa ruwa a jallo idan bai bayyana a babban kotun tarayyar Najeriya dake Kogi ba bisa zargin mallakar bindigogi ba bisa ka'ida

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta shigar da kara a babbar kotun tarayyar Najeriya dake Kogi domin tuhumar Sanata Dino Melaye da laifin baiwa wasu 'yan bangar siyasa biyu bindigogi.

Wadanda ake zargin Dino Melaye ya mika masu bindogin su ne Kabiru Saidu mai shekaru 31 da haifuwa, da Nuhu Salisu dan shekaru 25.

Tuhumar ta biyo bayan kama 'yan bangan ne da ake tuhuma da satar mutane da suka ce wani mutum ne mai suna Muhammad Audu ya hadasu da Sanata Dino Melaye a Abuja bara inda nan ne suka mallaki bindigogin.

Rashin bayyanar Dino Melaye gaban kotu, a zaman farko, ya sanya rundunar yin barazanar cewa matukar ya ki bayyana a gaban kotun ranar 28 ga wannan watan, zata ayyana shi a zman wanda take nema ruwa a jallo.

Kakakin rundunar Moshud Jimoh, a wata sanarwa ya ce sun aikawa shugaban majalisar dattawa halin da ake ciki saboda ya turo Dino Melaye din a yi masa tambayoyi amma ya ki.

Sai dai a martanin da ya mayar, Dino Melaye ya ce ba zai halarci kotun ba domin barazana ga rayuwarsa ake yi. Inji shi babu wanda ya taba zuwa gidansa a Abuja, ko a Kogi cewa ana nemansa ba. Ya yi zargin cewa wani shiri ne na neman hallaka shi.

Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da krin bayani

Your browser doesn’t support HTML5

Rundunar 'Yan Sanda Najeriya Ta Yi Barazanar Ayyana Neman Sanata Dino Melaye - 2' 26"