Rundunar ‘Yan sandan Jihar Borno Ta Kama Wasu Matasa 58

Kwamishinan 'Yan Sandan JIhar Borno Mohammed Aliyu

Rundunar ‘yan sandan jihar Borno ta gurfanar da wasu mutane 58 gaban manema labarai, wadanda ta ce ta kama bisa zargin aikata laifuka daban-daban ciki har da fyade da garkuwa da mutane.

Kwamishina ‘yan sandan jihar Borno, Mohammed Aliyu, ne ya gurfanar da mutanen, ya kuma bayyana cewa suna samin nasara ne sakamakon sabon shirin nan da suka fitar da ake kira “Operation Puff Adder.”

Akasarin wadanda aka kama matasa ne da shekarunsu suka fara daga 20 zuwa 35, ya yin da wasunsu suka kasance ‘dalibai, da ake zarga da aikata laifukan fyade da safarar miyagun kwayoyi da zamba cikin aminci da kuma fashi da makami.

Kwamishina Aliyu, ya ce nan bada dadewa ba za a gurfanar da mutanen gaban kotu domin doka ta yi halinta game da laifukan da ake zarginsu da aikatawa.

Wakilin Muryar Amurka Haruna Dauda, ya sami zantawa da wasu daga cikin wadanda ake zargin, inda wasunsu suka bayyana masa irin laifukan da suka aikata.

Domin cikakken bayani saurari rahotan Haruna Dauda.

Your browser doesn’t support HTML5

Rundunar ‘Yan sandan Jihar Borno Ta Kama Wasu Matasa 58 - 3'43"