Kwamandan rundunar STF a jahar Pilato, manjo janar Augustine Agundu ya ce, wadanda suka kaman, sun hada da yan fashi da makami da barayin shanu da masu garkuwa da mutane don neman kudin fansa da kuma yan kungiyar asirim sai kuma wani da suke zargi dan kungiyar Boko Haram ne.
Augustine Agundu ya ce jami’ansa sun kame Ya’u Mohammed babban dan fashi da makami a garin Toro, jihar Bauchi in da shi da tawagarsa su ka yi kwantan bauna wa sojoji suka harbe daya daga cikin sojojin a yankin Riyum.
Ya kara da cewa rundunar sun kuma kame wani Ishaku Pam wanda ya yi kaurin suna akan satar shanu a karamar hukumar Barikin Ladi.
Agundu ya kuma ce sun kama Isa Abdulladi, Usman Abdulkarim da Hassan Shu’aibu da zargin satar shanu, sannan wasu Musa Adamu, Ibrahim Musa da Alhassan Ahmed ana zargin su da hannu wajen kai hari a kauyen Kulben a kwanakin baya da ya kaiga asarar rayuka 12.
Sauran wadan da rundunar ke zargi da laifukan fashi da makami sun hada da Emmanuel Ebube, Tinchan Kumen, Solomon Dadong da wasu da aka kame laifin shiga kungiyar asiri suna cin zarafin al’umma.
Ya bayyana cewa an kama Umar Musa Tela da ake zargin dan dan Boko Haram ne wanda ya ce ya gudo ne daga garin Damagum a jihar Yobe sakamakon matsi na ‘Operation Lafiya Dole’.
Domin Karin bayani a saurari rahoton wakiliyar muryar Amurka Zainab Babaji:
Your browser doesn’t support HTML5