Rundunar Tsaron Najeriya Ta Jaddada Niyyar Murkushe Boko Haram

Hotunan Mukadashin Sufeton Yan Sanda da Kwamandan Runudnar Tsaro Ta musamman A Maiduguri

Rundunar tsaron Najeriya ta bayyana cewa, a wannan karon gwamnati ta zage damtse da kara damarar ganin bayan kungiyar Boko Haram, da kuma tabbatar da zaman lafiya mai dorewa a yankunan da ake fama da tashe tashen hankali sakamakon hare haren kungiyar Boko Haram

Rundunar tsaron ta bayyana haka ne yayin liyafar bukuwan sallah da aka shiryawa wadanda suke zaune a sansanan ‘yan gudun hijira na cikin gida.

A jawabinsa, kwamandan rundunan sojin sama na 153 dake Yola, Air Commodore Mohammed Yusufu, ya yaba rawar da babban hafsan sojin sama ke takawa dake zaburar da na kasa don fuskantar yan ta'adda.

Shima a nashi jawabin ga askarawan saman babban hafsan sojin saman Najeriya, Air Marshall Saddique Abubakar, yace gwamnati ta kuduri aniyar shawo kan wannan matsalar baki daya a wannan karon.

Yau dai fiye da shekaru goma ke nan da yan kungiyar Boko Haram ke kai hare hare a wasu sassan Najeriya da kuma wasu kasashen dake makwabtaka da Najeriyan, da ya zama sanadin asarar dubban rayuka baya ga wadanda ke gudun hijira da kuma asarar dukiya.

Saurari cikakken rahoton Ibrahim Abdul’aziz

Your browser doesn’t support HTML5

Rundunar tsaro ta lashi takobin shawo kan Boko Haram-3:30"