Rundunar Tsaron Farin Kaya NSCDC Ta Kama Mutane 848 da Suka Aikata Laifuka

Shugaban NSCDC a Borno Abdullahi Ibrahim

Cikin shekarar 2016 rundunar ta tsaron farin kaya ko NSCDC a takaice ta kame mutane 848 da suka aika muggan laifuka da suka hada da fyade, fashi da makami, satar shanu, da ta'adancin Boko Haram da fasa bututun mai da kera bama-bamai da dai sauransu.

Kwamandan rundunar na jihar Borno Abdullahi Ibrahim shi ya shaidawa manema labarai a birnin Maiduguri fadar gwamnatin Borno.

Acewar Abdullahi rundunar ta samu nasarori da dama wajen kame wasu bata gari da kwato wasu kudaden da suka haura nera miliyan sittin da biyar daga wasu mutane cikinsu har da wasu 'yan kungiyar asiri da 'yan damfara da aka sani da 419.

Ta bakin Abdullahi Ibrahim sun yi kokari sun kai wasu da suka kama kotuna inda suka samu nasara akan mutane 159. Suna da mutane 217 yanzu a hannunsu.

Dangane da wadanda suka kawo masu kara su ma sun samar masu kudadensu miliya 29. Sannan suna bin sawun nera miliyan 35.

Gurbatattu kayan abinci da NSCDC ta cafke a jihar Borno

Baicin laifukan da ya lissafa su kan kama mutanen dake yiwa mutane alkawarin samar masu aiki da zummar su yaudaresu. Akwai kuma batun zamba cikin aminci. Sun kuma kama kayan abinci gurbatattu.

Ga rahoton Haruna Dauda da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Rundunar Tsaron Farin Kaya NSCDC Ta Kama Mutane 848 da Suka Aikata Laifuka - 3' 45"