Hedkwatar dake Abuja tace ta samu nasarar kawar da wani hari da kungiyar Boko Haram tayi yunkurin kaiwa birnin Maiduguri.
Sanarwar da aka aikewa manema labarai ta samu sanya hannun babban jami'in soji mai kula da hulda da jama'a Manjo Chris Olu Kolade. Yace sojojin sun fatattaki 'yan kungiyar tare da kwace makamai da dama. Cikin makaman har da motocin sulke guda biyu da motoci kiran hilux guda goma sha bakawai. Sun hallaka maharan da dama.
Manjo Kolade ya kara da cewa sojojin da suka ji rauni ana yi masu jinya. Sun kuma cigaba da farauto maharan da suka tsere. Yace suna samun nasarar ne sakamakon hadin gwiwa da sojojin Kamaru, Chadi da Nijar.
A wannan harin na biyun ne aka samu rahotannin cewa wasu mutane 17 sun gamu da ajalinsu sakamakon fada masu da wasu makaman sojoji suka yi a gidajensu.
Gwamnan jihar Borno Shettima ya aika da sakon ta'aziya tare da jajantawa al'ummar da bala'in ya shafa kana ya jinjinawa sojoji da matasa 'yan sa kai da ake kira kato da gora sabili da jajircewa da suke yi. Yayi alkawarin tallafa masu.
Ga rahoton Haruna Dauda Biu.
Your browser doesn’t support HTML5