Suka ce muddin idan da gaske ake yi to mataki na gaba shine bada damar samar da kungiyoyi.
Firayim Ministan kasar ce Prayut Chan-o-cha shi ne ya bada wannan umurnin na kawo karshen zaman wannan kotun sojan, musammam akan laifukan dake da nasaba da harkokin tsaron cikin gida,da kalaman batanci ga gwamnati wanda ka iya tunzura jama’a da kuma zubar da martaban gidan sarautar Thai.
Jim kadan da darewa kan karagar mulki a cikin watan Mayu na shekarar 2014 Sojojin kasar sun kafa dokar ta baci, amma kuma tawagar sojojin da suka kira kansu kwamitin samar da zaman lafiya da bin doka da oda ta karfafa dokar wucin gadi wanda hakan ya bada damar yiwa ‘yan kasa hukunci ta kotun soja.
Kuma tun daga wannan lokacin ne, kotun ta soja ta saurari kararraki har sama da 1500 wanda suka kunshi mutane sama da 1,800 a dukfadin kasar, kuma kusan dukkansu masu alaka da batun makami ne.
Angkhana Neelapaichit wanda dan hukumar kare hakkin bil adama ne a kasar yace duk da yake hukumar tayi na’am da wannan mataki da gwamnati ta dauka to amma akwai bukatar gwamnatin ta kara karfafa karehakkin bil Adama.