Likitocin rundunar sojojin saman Najeriya sun taimakawa 'yan gudun hijira a arewa maso gabas da magunguna da ayyukan tiyata daban daban a kokarin inganta lafiyarsu.
A cikin birnin Maiduguri kadai likitocin sun duba lafiyar 'yan gudun hijira sama da dubu casa'in. Haka ma sansanonin 'yan gudun hijira dake Dalori cikin jihar Bornon da Yola a jihar Adamawa sojojin sun yiwa 'yan gudun hijira fiye da dubu saba'in magani.
Sojojin basu tsaya nan ba domin sun zagaya sansanonin 'yan gudun hijra dake wurare daban daban a arewa maso gabashin Najeriya suna yi masu aikin tiyata ko basu magani.
Babban hafsan rundunar Air Vice Marshall Sadique Abubakar ya yi karin haske tare da ba da dalilan da suka sa suna aikin taimakon. A cewarsa suna ganin suna da hakkin su kare mutane su kuma taimakawa wadanda karewar ba ta yi tasiri. ta yadda basu fita kauyukansu ba sun zama 'yan gudun hijira. Injishi kwana kwanan nan mutanensa sun yi aiki tiyata wa mutane fiye da 133. Sun yiwa masu kaba aiki da kuma masu yanar ido.
Shi ko kakakin sojojin Olatokunbo Adesanya ya ce hikimar taimakon domin janyo mutanen da rikicin Boko Haram ya rutsa dasu ne jiki. Ya ce abu ne da yake da mahimmanci kwarai. Yakamata mutanen da suke taimakawa su gane sojojin 'yanuwansu ne kuma suna bukatar hadin kansu, wanda zai taimakawa rundunar a gumurzun da ta keyi da 'yan ta'addan Boko Haram.
Dr. Saleh Abba jagoran kungiyar Smile Medical Mission, tawagar wasu likitoci dake kula da wadanda rikicin Boko Haram ya rutsa dasu da kuma suke aiki kafada da kafada da likitocin sojojin saman Najeriya, ya ce lokacin da suka je garin Bama ba bu asibiti ko daya. Sojojin ne suka fara kafa asibiti a garin. A wasu wuraren sojojin na aikin tiyata kamar na kaba da yanar idanu,
Ga rahoton Hassan Maina Kaina da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5