Rundunar sojojin Najeriya ta kaddamar da wani gagarumin yaki da masu sace sacen dabbobin al’umma tare da sace mata da yara da kuma kona gidajen jama’a, domin kakkabe miyagun mutanen dake sansani cikin dazuzzukan jihar.
Kamar yadda ministan tsaro na Najeriya Mansur Dan Ali ya bayyanawa wakilin sashen Hausa na muryar Amurka Umar Faruk Musa, ya bayyana cewa wannan gagarumin aiki da aka fara a jihar zamfara zai sami karramawar ziyarar shugaba Muhammadu Buhari a gurin wannan aiki.
Ana sa ran kammala wannan yaki da wadannan miyagu daga sati guda zuwa wata daya, ministan ya bayyana cewa an dade ana fama da wadannan miyagu amma duk da sauran matsalolin da ake fama da su a fadin kasar amma wannan lokaci kam za’a yita ta kare.
Ya kuma kara da cewa rahotanni sun bayyana cewa an sami labarin cewa wasu daga cikin barayin sun fara gangarawa zuwa wasu makwabtan kasashe amma a cewar sa, za a yi kokari a datse hanyoyin domin tabbatar da kakkabe su daga wadannan wurare.
Ga rahoton Umar Faruk Musa.
Your browser doesn’t support HTML5