Rundunar Sojin Najeriya Ta Yi Karin Haske Game Da Zargin Tsare Dan Jarida A Fatakwal

Wata sanarwa dauke da sa hannun daraktan hulda jama’a na bataliyar, Laftanar Kanar Danjuma Jonah Danjuma ta ce kamen nasa nada nasaba da samamen da ake gudanarwa a yankin Neja Delta na yaki da satar danyen mai.

Shelkwatar, bataliya ta 6, ta rundunar sojin Najeriya, ta bayyana damuwa game da zarge-zargen da ake yadawa a kafafen sada zumunta na cewa ta tsare wani dan jarida mai binciken kwa-kwaf a birnin Fatakwal.

Wata sanarwa dauke da sa hannun daraktan hulda jama’a na bataliyar, Laftanar Kanar Danjuma Jonah Danjuma ta ce kamen nasa nada nasaba da samamen da ake gudanarwa a yankin Neja Delta na yaki da satar danyen mai.

Sanarwar ta ce "a wani samame da aka shirya, dakaru sun bi sawun batagarin zuwa wani wurin satar danyen mai.

“Yayin samamen, an kama mutane da dama, ciki har da Mr. Fisayo Soyombo, wanda aka tarar a wurin.

Fisayo Soyombo

“Ana gudanar da binciken farko a kan batagarin da aka kama a wurin, ciki har da Mr. Soyombo domin tantanace irin rawar da suke takawa a satar danyen man” a cewar bataliyar.

Bayanan sirri da aka samu a baya-bayan nan sun bankado ayyukan wani gungun batagarin da ya yi kaurin suna wajen lalata bututun mai a yankin.

Bataliyar ta yi kira ga kafafen yada labarai su tantance sahihancin rahotanni kafin su yada su ga jama’a.