A kokarin da su ke yi na kakkabe burbushin ‘yan ta’addan kungiyar Boko Haram da ake kira ISWAP a takaice, sabuwar rundur zaratan sojojin da aka kafa ta hadin gwiwa wato NASFC a takaice, wadda kuma ake kira Lafiya Dole, ta fatattaki ‘yan ta’addan da suka kai wa sansanonin soja farmaki a Baga.
Dakarun na musamman na bataliyar 707 da ake jinjinawa, wadanda kuma suka jagoranci kai ga cimma wannan gagarumar nasarar, su suka kai farmakin da ya fatattaki ‘yan ta’addan da yawa a wannan yankin, duk da cewa wasu marasa kishin kasa sun je sun gargadi mayakan kafin harin.
Dakarun na musamman sun fara kai farmaki ne a ranar 28 ga watan Disamban shekarar 2018, inda su ka kori mayakan daga garuruwan Zare, Gudumbali, Kukawa da Kross Kauwa ba tare da samun wata tirjiya daga mayakan ‘yan ta’addan ba.
Koda yake, a garin Kross Kauwa, ‘yan bindigar na ISWAP sun yi babban kuskuren fitowa. A wani tsari na kwarewa, dakarun sun yi amfani da damar da suka samu ta kai farmaki nan take, kuma suka yi nasara akan mayakan, sannan suka kwato wasu kayayyaki daga garesu.
Duk da cewa wasu daga cikin ‘yan ta’addan sun yi kokarin su kutsa sansanin sojan da ke Monguno, zaratan sojojin sun yi masu tarko, sannan suka fatattaki da yawa daga cikin mayakan, su ka kuma kwace bindigoginsu da yawa da harsasai.
Tuni dakarun da ke cike da kwarin gwiwa suka hade da sojojin dake Baga, inda suka kori ‘yan ta’addan a wani sansanin soja. Sai dai, a yayin da suke wannan kokarin, rundunar sojan ta yi rashin jami’i daya da soja daya, yayin da sojoji 5 suka jikkata. An riga an kwashe gawarwakin sojojin biyu da kuma wadanda suka jikkata daga wurin.
Sojojin da suka jikkata na samun sauki kuma ana masu jinya a asibiti. Yanzu haka dai dakarun na can na aikin kakkabe sauran mayakan da ke arewacin jihar Borno inda suke maida hankali akan yankin tafkin Chadi.
Dakarun na mussaman sun iya cimma wannan nasarar ne tare da hadin gwiwar sojojin saman Najeriya da suka samar da bayannan sirri, suka kuma taimaka ta kai hare-hare ta sama ta hanyar yi wa mayakan na ISWAP kawanya.