Rundunar Sojin Najeriya Ta Ce Ta Kuduri Aniyar Kawo Karshen Rashin Tsaro A Kasar

Rundunar Sojin Najeriya

Rundunar sojin Najeriya ta jaddada kwarewarta wajen kakkabe burbushin ‘yan ta’adda da sauran kungiyoyi dake tada kayar baya da barazana ga tsaro a kasar.

Hafsan hafsoshin Najeriya, Laftanar Janar Faruk Yahaya ya bayyana hakan ne a karshen gasan harba kananan makamai da runduna ta uku dake Jos ta karbi bakuncin sauran rundunoni bakwai dake fadin Najeriya.

Rundunar Sojin Najeriya suna karbar horo

Hafsan Hafsoshin, Faruk Yahaya ya ce horar da dakarun zai basu karin kwarewa don yaki da kawo karshen matsalolin tsaro a kasar.

Gasan harbe-harben ya hada da harba bindigar AK-47, karamar bindiga ta Pistil, Mashin gon da sauran kananan makamai.

Rundunonin da suka shiga gasar sun hada da runduna ta daya dake Kaduna, runduna ta biyu dake Ibadan, runduna ta uku dake Jos da runduna ta shida dake Patakwal.

Sauran sun hada da runduna ta takwas dake Borno, runduna ta tamanin da daya dake Legas sai runduna ta tamanin da biyu dake Enugu da shelkwatar rundunar sojin dake Abuja.

A karshen gasar, shelkwatar rundunar sojin na Abuja ta kasance ta daya a iya harbin makamai.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

Rundunar Sojin Najeriya Ta Ce Ta Kuduri Aniyar Kawo Karshen Rashin Tsaro A Kasar