Rundunar sojan Nigeria ta baiwa kungiyar yan sintiri da maharba a karamar hukumar Darazo jihar Bauchi arewa maso gabashin Nigeria kyautar naira miliyan daya domin karfafa musu gwiwa.
Rundunar soja ta bada wannan kyauta ne domin komarin da yan sntiri da maharba suka yi na ceyon wasu mutane maza da mata guda goma da aka sace aka boye a dajin Balmo dake karamar hukumar Darazo.
Hafsan sojojin Nigeria Janaral Yusuf Tukur Buratai ne ya bada kyautar kudin wanda kwamandan brigade ta 33 Janaral Dusu ya mika a madadin sa.
A jawabin daya gabatar, hafsan sojojin Nigeria ya yaba da namijin kokarin da yan sintiri suka nuna domin kubutar da wadanda aka sace.
Yace za'a karfafa musu gwiwa kuma rundunar soja tana neman hadin kan su domin sune 'yan gari.
Shugaban karamar hukumar Darazo Baba Dan Lawan Hamza ya baiyana godiya da gamsuwarsa a madadin yan karamar hukumar. Haka kuma yayi fatar Allah yasa a samu zaman lafiya a Nigeria.
Your browser doesn’t support HTML5