Rundunar Sojan Najeriya Na Neman Ahmed Salkida Da Wasu Mutane Biyu

Sauran 'yan matan Chibok da suka rage a hannun kungiyar Boko Haram

Biyo bayan fitowar wani sabon hotan bidiyo da Kungiyar Boko Haram tayi wanda ke dauke da 'yan matan Chibok da ta sace sama da shekaru biyu da suka wuce, iyayen wadannan yan mata sun fara bayyana ra’ayoyinsu, yayin da suma masana harkar tsaro ke tsokaci.

‘daya daga cikin iyayen ‘yan matan Mr. Ayuba Chibok, ya nuna jin dadinsa kan cewa har yanzu akwai sauran ‘yan matan da rai, har ma kuma anji muryar ‘daya daga cikin su.

Sa’o’i kadan bayan fitar sabon hotan bidiyon, rundunar Najeriya ta ce tana neman ‘dan jaridar nan Ahmed Silkida wanda ke da kusanci da kungiyar Boko Haram ruwa a jallo. Hakan nan ma Sojojin na kuma neman Ambasada Ahmed U. Bolori da kuma Barista Aisha Wakil, wanda rundunar ta ce suna dauke da wasu bayanai masu muhimmanci kuma sunki su baiwa hukumomi.

Fatan iyayen ‘yan matan dai shine a hanzarta a sakar musu da ‘ya’yansu domin kar rayuwa ta salwanta.

Domin karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Rundunar Sojan Najeriya Na Neman Ahmed Salkida Da Wasu Mutane Biyu - 3'39"