Rundunar Tsaron Farin Kaya Ta Kubuto Wasu Mutane Da Aka Yi Garkuwa Da Su

Kwamandan Sibil Defens na Nasarawa

Hukumar tsaro ta farar hula a jihar Nasarawa ta yi nasarar kwato wasu mutane bakwai da barayi suka yi garkuwa da su, a lokacin da barayin suka tare matafiya, a makon jiya, ciki har da mataimakin gwamnan jahar, Dakta Emmanuel Akabe.

Kwamandan rundunar tsaro ta farar hula Civil Defence a jihar Nasarawa, Muhammad Gidado Fari ya ce ‘yan kundunbalar hukumar ne suka ceto wadanda aka yi garkuwa da su, sai dai masu garkuwan sun arce da gudu kafin jami’an nasu su isa dajin.

Daya daga cikin wadanda aka ceton ya ce sun sha azaba na tafiya mai nisa cikin daji da rashin abinci, hatta ma sai da suka biya kudin fansa.

A halin da ake ciki dai rundunar ‘yan sandan jahar Nasarawa ta ce ta damke mutane uku da ta ke zargi da fashi da makamin da yayi sanadin mutuwar jami’anta uku da ke tsaron lafiyar mataimakin gwamnan jihar da wasu mutane biyu.

Zainab Babaji na dauke da Karin bayani a cikin wannan rahoto:

Your browser doesn’t support HTML5

AN KUBUTAR DA MUTANE DAGA MASU GARKUWA