Rundunar Safe Haven Ta Kubutar Da Wasu Mutane Da Kuma Cafke Barayin Mutanen

A wata ziyara da ya kai jihar Bauchi kwamandan rundunar Safe Haven, Manjo Janar Nicolas Ibe, ya shaida cewa jam’an sa sun sami nasarar kubutar da wasu mutane da kuma damke wadanda suka yi garkuea a mutanen domin neman kudin fansa.

Mai ba gwamnan jihar Bauchi shawara akan harkarkokin tsaro janar Ladan Yususf mai ritaya, a Karin hasken da yayi akan ‘yan bata garin ya bayyana cewa aikin hadin gwiwar da suke samu tsakanin sojoji da ‘yan sanda da kuma ‘yan danga, kwalliya na biyan kudin sabulu.

A halin da ake ciki, shugaban kungiyar Danga security na karamar hukumar Toro Yusuf Abdullahi, ya ce sun sami nasarar ceto wasu mutane shidda ciki harda mata daga hannun masu garkuwa da mutanen kuma sun sami nasarar damke bakwai daga ciki.

Daga karshe shugaban kungiyar ‘yan dangar ya kara da cewa sun sami hadin kan jami’an sojoji, sai dai ya yi kira ga gwamnatin jihar data taimaka masu da kayan aiki domin su kakkabe wadan nan bata gari dake satar shanu da yin garkuwa da mutane domin kudin fansa da suka gallabi jihar, domin a cewar sa, yawanci su da kawunan su suke daukar dawainiyar yin wasu abubuwan da dama.

Domin Karin bayani, saurari rahoton Abdulwahab Muhammed.

Your browser doesn’t support HTML5

Rundunar Safe Haven Ta Kubutar Da Wasu Mutane Da Kuma Cafke Barayin Mutanen