Rundunar tace tayi haka ne da niyyar zakulo wadanda suka fasa bututun man na yankin Niger Delta, kamar yadda darektan yada labarai na hedikwatar tsaron Nigeria Birgediya Janar Rabe Abubakar ya shaidawa wakilin sashen Hausa Hassan Maina Kaina.
‘’Wadanda suka yi wannan abu ko wanene shi ko kuma ko wanene su, ina tabbatar wa Jamaa cewa za a kama su kuma a hukunta su kamnar yadda dokar kasa ta tanada, domin wasu ‘yan tsirari ne keson mayar da hannun agogo baya domin ba wani jamiaan tsaro da zaice a bar ko su wanene suci gaba da abinda suke yi’’.
Janar Abubakar yace yana kallon tsagerun na yankin Niger Delta a matsayin ‘yan taadda kuma zasu dandana kudar su.yaci gaba da cewa.
‘’Abinda suke yi taaddanci ne kuma ba zamu bar su ba kuma duk wanda yayi wani abu muna nan muna bincike, muna nan muna shiga cikin kauyuka domin ganin cewa mun kare duk wani dukiyar gwamnati ko ta mai ne koba ta mai ba, kana muyi ainihin kare wadanda ba ruwan su da wadanda ba ruwan su da wannan al'ama’in da wakana a wannan yankin’’.
Ga Hassan Maina Kaina da Karin bayani
Your browser doesn’t support HTML5