Rufe Iyakar Nijar Da Najeriya Da ECOWAS Ta Yi Ya Haifar Da Matsin Rayuwa

Mahalarta Taron Kudi Na Ecowas A Lagos

BIRNIN NKONNI, NIGER - Yayin da juyin mulkin Nijar na 26 ga watan Yuli, wanda sojoji suka hambarar da gwamnatin shugaba Muhammad Bazoum ke shiga watanni uku, mazamna iyakar Nijer da Najeria su na ci gaba da kururuwar shiga matsi a sakamakon takunkumin da kungiyar raya Tattalen Arzikin kasashen yammacin Nahiyar Africa ECOWAS ko CEDEAO ta kakabawa kasar, musaman kange iyakokin kasar da kasashen dake makwabtaka da kasashen ECOWAS ko CEDEAO suka wa Nijer.

Wakilin Muryar Amurka a birnin N'Konni Harouna Mammane Bako ya nemi jin ta bakin mazauna al'ummomin da ke kan iyakar kasashen biyu. Alhai Ali Mamani mazaunin karamar hukumar Illela a jihar Sakwato ne a Najeriya kuma ga abin da yake cewa : radadi kam mun ji shi, duk wani matashi mazanunin NKonni mai harkar shige da fice, wannan rufe bodar bamu ji dadin shi ba, sai dai ace an gode Allah.

Amma mu fatanmu shi ne Allah ya bai wa mahukuntanmu ikon sasantawa su bude bodar nan, domin ta nan muke samun na abinci, maza da mata, babba da yaro , mun san Allah ya na ikon yin duk abinda ya so. Domin ni yanzu da ka ganni in banda harkar shige da fice bani da wata hanyar samun na abinci kuma tun ranarda aka rufe kan iyaka babu abinda na yi.

Suma, wadansu al'ummar Nijar dake bangaren birni N'Konni a Jahar Tahoua, suma sun koka saboda halinda suka samu kansu. Mai magana na farko Muhammadu Rahou yace dukkanin wani al'amari daga Allah yake kuma babu wanda yake da ikon janyowa wani mahaluki wata wahala.

Abun da muke kokawa da shi a matsayin mu na talakawa shine batun farashin abinci da yayi tashin gworon zabi. shi kuma mai magana na gaba cewa yayi, 'yan kasuwa tsakanin Nijar da Najeriya, kowa ya ji a jikin shi tsawon wattannin na da aka yi, gaskiya akwai matsaloli sossai musamman ma ga 'yan kasuwa, kowa ya samu matsi.

Su ma, yan Najeriya dake bangaren Najeriya a karamar hukumar Illela ta jahar Sokoto, sun ce yankin ya fada cikin matsala babba sanadiyyar rufe kan iyakokin Nijar da kasashe mambobin ECOWAS su ka yi.

Duk dai yadda ake ciki, wannan rufe iyakar musaman ta Najeriya, ya janyo tasgaro ga tattalin arzikin kasashen biyu, akan wannan iyakar, tare da jefa masu hada - hadar kasuwanci cikin halin sai wada hali yayi, yayin da sauran yan kasar ke kira a dai jure.

A saurari cikaken rahoton Harouna Mamman Bako:

Your browser doesn’t support HTML5

YAN NIJER DA YAN NAJERIYA DAKE KAN IYAKA SUN SOMA JIN RADADIN RUFE IYAKAR NIJER GA JIKIN SU.mp3