Rufe Bankuna: Ana Amfani Da Tsarin Ba Ni Gishiri In Ba Ka Manda A Mubi

  • Ibrahim Garba

'Yansandan Najeriya wajen aikin tabbatar da tsaro don a samu gudanar da harkokin yau da kullum.

Rashin bude bankuna a yankin Mubi da kewaye ya sa an shiga amfani da tsarin ba ni gishiri in ba ka manda a hadahadar cinakayya, al'amarin da ke cike da hadari

Da yawa daga cikin wadanda su ka bar yankin Mubi saboda hare-haren Boko Haram sun dawo tun bayan da sojojin Najeriya su ka fatattaki mayakan sa kan. To amma har yanzu akwai wasu matsalolin da ke addabar yankin.

Duk kuwa da cewa garin Mubi shi ne birni na biyu a girma da yawan jama’a a yankin kuma mai dauke da kasuwa mafi girma a yankin arewacin jahar kuma gashi ba ta da nisa sosai daga kan iyakar kasar Kamaru. Duk da haka, bankunanta har yanzu a rufe su ke, abin da ya tilasta mutanen kananan hukumomi 6 na yankin ciki har da shi kansa garin mubi cikin matsalar hadahada. Mutanen wadannan kananan hukumomin su kan shafe tafiyar kimanin kilomita 350 zuwa Yola inda bankuna su ke. Wannan al’amarin na illa sosai ga harkar gwamnati da kasuwanci da sauran al’amuran yau da kullum, a cewar wakilinmu Sanusi Adamu shugaban ‘yan kasuwa na Mubi Kwamrad Abdulkadiri Musa ya gaya masa cewa ayanzu ‘yan yankin sun shiga amfani da tsarin bani-gishiri-in-baka-manda tamkar zamanin jahiliyya. Ya ce wannan ya sa an shiga amfani da dabaru masu kasada sosai ciki har da kwace kudaden mutane a hanya.

Shi ma Sarkin Tiken Mubi, Alhaji Rabiu ya ce rashin bankunan ya sa da dama daga cikin masu hulda da kasuwa sun kaurace, ciki har da Ibo. Y ace yanzu kashi daya cikin dari ne kawai na kasuwar ke ci. Hatta ma’aikatan yankin sun shaida ma Sanusi Adamu cewa sai sun dauki kimanin kwanaki uku kafin su samu albashinsu ko ma bayan sun yi tafiya mai nisa zuwa Yola.

Your browser doesn’t support HTML5

Rufe Bankuna: Ana Amfani Da Tsarin Ba Ni Gishiri In Baka Manda A Cinakayyar Mubi-3'28''