Rufe Bakin Iyakokin Najeriya Ya Haddasa Tsadar Rayuwa

Alkalumman hukumar kididdiga a Najeriya sun bayyana yadda farashin kayan abinci suka hauhawa a kasar.

Kididdigar ta kuma nuna raguwar masu sayan kayan, lamarin da ya fi tsanani a shekaru 4 da su ka wuce.

A watan Oktoban da ya gabata ne farashin kayayyakin suka karu da kashi 11.61%, wanda ya haura na watan Satumba da ya tsaya a kashi 11.24%.

Masana tattalin arziki dai na alakanta lamarin da rufe iyakokin Najeriya da gwamnatin kasar ta yi.

Iyakar Birnin Legas da Jamhuriyar Benin

Sun ce akwai riba da faduwa ta wani bangaren na rufe iyakokin, amma ba za a ga tasirin sauki ba matukar an bar kasuwa ta yi halinta.

Hukumar hana faskwauri ta Najeriya ce ta sanar da rufe iyakokin a cikin 'yan watannin da suka gabata, domin hana shigowa da dukkan kayan masarufi sai abun da hali ya yi nan gaba.

Wannan matakin da gwamnatin ta dauka dai ya janyo ce-ce ku-ce sosai, inda mutane da dama suke bayyana yadda hakan ya shafi kasuwancinsu, ya kuma janyo hau-hauwar farashin kayyiyaki da dama.

Shugaban hukumar fasakwauri Kanar Ibrahim Hameed Ali

Shugaban hukumar Kanar Hamid Ali shi dai ya ce sun yi hakan ne don hana fasakwauri ne da kuma inganta lamuran tsaro.

Ga wakilinmu, Nasiru Adamu El Hikaya da karin bayyani.

Your browser doesn’t support HTML5

Rufe Bakin Iyakokin Najeriya Ya Haddasa Tsadar Rayuwa 2'10"