Roof Yace Har Yanzu Yana Kan Bakansa Akan Zama Lauyan Kansa

Dylann Roof wanda ke huskantar hukuncin kissa na kashe wasu mutane 9 bakaken fata a wata cocin birnin Charleston dake jihar Carolina ta Kudu, ya fadawa alkali cewa baida niyyar kiran ko wane shaida kuma ba zai gabatarda wata hujjan aikata wannan danyen aiki ba, idan anzo wajen yanke mishi hukunci.

Roof ya fada jiya laraba cewa har yanzu yana kan bakansa akan cewa shine zai kasance lauyan kansa, idan a fara shara’ar a cikin sati mai zuwa, sai dai alkali Richard Gergel yace Roof na iya sauya raayin sa.

Roof dai ya jima yana zaman lauyan kansa tun bayanda ya kori lauyoyin dake kare shi, tun bayan da masu yanke hukunci suka same shi da aikata laifuffuka har 33 dake da nasaba da nuna kyama ga wani jinsi na al’umma da kuma hana wa doka aiki.

Lauyyin Roof suka ce suna kyautata zaton ya sallame su ne saboda yana ganbin kamar zasu gabatarda wata shedar da zata tozarta shi,wadda kuma watakila alkalin ya yi anfani da ita domin ceton rayuwar sa.