WASHINGTON, D.C. —
Cristiano Ronaldo dan wasan kungiyar Juventus, na fatan cewar zasu fitar da kungiyar Athletico Madrid a haduwarsu na biyu cikin gasar cin kofin Zakarun Turai ranar Talata.
A karawarsu ta farko Athletico ce ta samu nasara akan Juventus daci 2-0 a Spaniya, inda Gimenez da kuma Diego Godin suka zura mata kwallaye a fafatawar da suka yi a cikin watan Fabrairu 2019.
Dan wasan na tawagar kwallon kafar kasar Portugal Ronaldo ya ci Atletico kwallo 22 a wasa 31 a lokacin da yake Real Madrid, ciki har da wanda ya ci a bugun daga kai sai maitsaron gida Penalty a 2016.
Ronaldo yace zasu yi iya kokarinsu domin kai wa zagayen gaba. Za'a buga wasanni da misalin karfe 9 na yammaci agogon Najeriya, Nijar, Kamaru da kasar Chadi.