Romney ya gana da Firai Ministan Isra'ila

Dan takarar Republican Mitt Romney

Dan takarar shugaban kasar Amurka Mitt Romney ya fara wata gajeriyar ziyara a Isra’ila yau Lahadi

Dan takarar shugaban kasar Amurka Mitt Romney ya fara wata gajeriyar ziyara a Isra’ila yau Lahadi tare da ganawa da dadadden abobinshi Firai Minista Benjamin Netanyahu, wanda ya shaidawa Romney cewa, yana ya yarda da matsayin jam’iyar Republican kan cewa, babban hadarin da ke gaban kasashen duniya, shine yunkurin Iran na samun makamin nukiliya.

Romney yace yana son yaji ra’ayin Mr. Netanyahu a kan yiwuwar kara daukar wadansu matakai domin shawo kan Iran a tunaninta na mallakar makaman nukiliya.

Romney zai kuma gana da Firai Ministan yankin Paladinawa Salam Fayyad a birnin Kudus.

Romney ya isa Isra’ila jiya asabar da dare daga Birtaniya, inda ya halarci taron bude gasar wasannin Olympic. Zai wuce zuwa kasar Poland gobe Litinin, kasa ta karshe da zai yada zango a ziyarar tashi.