Ana Ci Gaba Da Jimamin Rasuwar Roger Moore "James Bond-007"

FILE - British actor Roger Moore, playing the title role of secret service agent 007, James Bond, is shown on location in England in 1972. Moore, played Bond in seven films, more than any other actor. Roger Moore's family said Tuesday May 23, 2017 that t

Jarumin da ya fi kowa yawan fitowa a matsayin dan leken asiri James Bond ko "007" Roger Moore, ya rasu yana da shekaru 89 da haihuwa.

Ana ci gaba da bayyana jimamin rasuwar fitaccen jarumi dan kasar Ingila, Roger Moore, wanda ya fi shahara a zaman dan leken asiri mai lamba 007 a fina-finan James Bond, wanda kuma ya rasu jiya talata yana da shekara 89 da haihuwa.

A jiya talata ne 'ya'yansa suka bayar da wata sanarwa suna bayyana rasuwar Sir Roger Moore a kasar Switzerland, a bayan da yayi fama na dan gajeren lokaci da cutar sankara.

Babban darektan Asusun Tallafawa Yara Na Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF, Anthony Lake, ya bayyana mutuwar Sir Roger Moore a matsayin "babbar hasara ga duniya ta mutumin da ya jajirce wajen kare muradun yara na duniya, yayin da dukkanmu a nan asusun UNICEF muka yi hasarar babban aboki."

Iyalan marigayin sun ce a bisa wasiyyar da ya bari, za a yi jana'izarsa a Monaco, amma ba za a gayyaci baki ba.

Moore ya shahara a fadin duniya daga shekarar 1973 zuwa 1985, a lokacin da yafito a zaman jarumi a fina-finan sanannen dan leken asiri James Bond, ko 007, har guda bakwai, cikinsu har da "Live and Let Die" da kuma "The Spy Who Loved Me."