Rikicin Zamfara: Sarakunan Gargajiyar Jihar Sun Ce Zasu Fasa Kwai

A ‘yan kwanakin baya ministan tsaron Najeriya Mansur Dan Ali, yayi zargin cewa akwai wasu manyan sarakunan gargajiya a jihar Zamfara dake hulda da ‘yan bindigar jihar masu kai hare-hare da satar mutane don neman kudin fansa, lamarin da ya fusatar da sarakunan jihar har suka fito suka kalubalanci ministan akan ya fito fili ya bayyana wadanda yake zargi suna da hannu a lamarin.

Mai martaba sarkin Anka, Alhaji Attahiru Ahmed, shugaban majalisar masarautu ta jihar, ya ce har yanzu suna nan kan bakan su wajen kalubalantar ministan da ya bayyana sarakunan da ake zargi da mu’amulla da ‘yan bindigar.

Mai martaban yace kamata yayi ministan ya zo ya ja kunnen sarakunan ko ya fadi abubuwan da suka yi, ya kara da cewa idan aka tura su bango zasu fasa kwai.

To sai dai a nata bangaren, gwamnatin jihar Zamfara, zargin ta akan sarakunan ya sha bam-bam da na ministan a cewar kwamishinan lamuran kananan hukumomi Bello Muhammed Dankande.

Tuni dai gwamnatin tarayya ta dakatar da ayyukan hako ma’adinai a jihar Zamfara, a daidai lokacin da rundunar sojan sama ta kaddamar da lugudan boma-bomai a maboyar ‘yan bindigar a jihar.

Ga karin bayani cikin sauti daga Muratala Faruk Sanyinna.

Your browser doesn’t support HTML5

Rikicin Zamfara: Sarakunan Gargajiyar Jihar Sun Ce Zasu Fasa Kwai - 2'48"