Rikicin Ya Barke A Wajen Zaben Cike Gurbi A Kasar Ghana

shugaban jam'iyar NPPt

Manyan jam'iyun siyasa a kasar Ghana suna tsirawa juna hannu kan tashin hankalin da ya biyo bayan zaben cike gurbi da aka gudanar a mazabar Talensi inda mutane da dama suka ji rauni.

Al’ummar kasar Ghana suna Allah wadai da rigingimu da suka tashi wurin zaben cike gurbi da akayi a Mazabar Talensi shine yayi sanadiyar wasu harbe-harbe tsakanin matasan jami’iyar NDC mai mulki da na babban jami’iya hamayy ta NPP inda mutane dama suka ji rauni.

A ranar Talata ne hukumar zabe ta shirye zaben cike gurbi wanda tsohon dan majalisa na Talensin na jam’iyar NPP mai hamayya Masori ya bari, inda dan takarar jam’iya mai mulki Miti Baba, ya lashe zabe da kashi kuri’u arba’in da biyu da dukan kuri’un da aka kada.

A daidai lokacin da ake kirga kuri’un ne wadansu matasa suka ba hammata iska, harda harbe harbe saida ‘yan sanda suka kai dauki kafin a iya shawo kan lamarin.

Jam’iyun dai suna dorawa juna alhakin lamarin. Yayinda ‘yan siyasa suke tsirawa juna hannu dangane da lamarin, al’ummar kasar Ghana sun yi kira ga ‘yan siyasa su rika hakuri da juna, tare da kira ga hukumomi su hukumta dukan wadanda ake kamawa da tada zaune tsaye domin gudun kada kasar ta tsunduma cikin rikicin siyasa kamar yadda ake gani a wadansu kasashen Afrika.

Ga cikakken rahoton da wakilinmu Baba Yakubu Makeri ya aiko mana.

Your browser doesn’t support HTML5

Rahoton Tashin Hankali a Kasar Ghana-2:55