Wannan kuma na zuwa ne yayin da jam’iyar APC a jihar Adamawa ke fama da rikicin cikin gida game da zaben fidda gwani.
Da alamun dai akwai ‘yan kallo a zaben shekarar 2019, ganin cewa tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku, shine yanzu dan takarar shugaban kasa, a inuwar babbar jam’iyar adawa ta PDP, yayin da ake ganin zai yi kokarin ganin ya samu nasara a jihar sa ta Adamawa, jihar da jam’iyar APC ke mulki a yanzu.
Ko a kwanaki, a wajen wani gangami a Yola, Atiku ya sha alwashin sai ya kawo jiharsa, inda ya ce sun san inda zasu kwance kurar da suka daure tun farko.
To wai ko anya cikin gwamnatin jihar bai dubi ruwa ba kuwa da zaman Atiku dan takarar PDP ayanzu? Kwamared Ahmad Sajo, dake zaman kwamishinan yada labaran jihar, ya ce ai su ko a gyalensu.
To sai dai kuma wannan na zuwa ne yayin da fusatattun yayan jam’iyar APC a jihar dake kokawa da yadda aka gudanar da zaben fidda gwani na gwamna a jihar, ke cewa muddin uwar jam’iyyar bata soke zaben ba, to kuwa su shinkafa da wake zasu yi a zaben 2019.
Domin karin bayani saurari rahotan Ibrahim Abdul’aziz.
Your browser doesn’t support HTML5