Rikicin Pakistan-India Ya Lakume Rayukan Farar Hula Hudu

Pakistan ta ce dakarun India sun yi harbe-harbe a tsallaken yankin Kashmir da ke tsakanin iyakarta da India, wanda ake kira LOC a takaice, inda farar hula hudu suka mutu wani kuma ya jikkata.

Wata sanarwar da rundunar sojin Pakistan ta fitar da yammacin ranar Laraba ta ce India ta saba yarjejeniyar tsagaita wutar da bangarorin biyu suka amince da ita.

A cewar Pakistan Indiar ta tsiri harbe-harbe akan kauyukan da ke karkashin ikon Pakistan a yankin ba tare da wata tsokana ba.

Sanarwar ta kuma kara da cewa dakarun Pakistan sun maida martanin harbin da India ta yi.

Sai dai nan take dai jami’an India ba su yi wani bayani kan wannan lamari ba.