Rikicin Manoma Da Makiyaya: An Hori ‘Yan Jarida Kan Rahotannin Kawo Salama

  • Ibrahim Garba

Wasu barayin shanu da aka kama

A cigaba da ake na shawo kan zub da jinin da ke yawan faruwa tsakanin manoma da makiyaya, an horar da 'yan jarida kan yadda za su iyamma bakinsu da kuma yin adalci a duk lokacin da rigima ta barke tsakanin manoma da makiyaya, da yanayin rayuwarsu ke sa su na yawan gamuwa. Wataran a rabu cikin raha, watan ran jina-jina.

Ganin yadda manoma da makiyaya a Najeriya ke yawan fada, wata kungiyar rajin tabbatar da zaman lafiya ta kasa da kasa mai suna “Search for Common Ground” a Turance, ta shirya ma ‘yan jarida taron ankarar da su muhimmancin bayar da rahotannin da za su kai ga zaman lafiya da cigaba musamman tsakanin manoma da makiyya.

Taron ya lura cewa matsalar makiyaya da manoma a wannan marrar ta zarce batun katse burtaloli da lalata amfanin gona ta kai ga kashe-kashen rayuka da barnata amfanin masu yawan gaske, wanda hakan ya janyo karancin abinci da talauci da kuma yawan zama cikin tsoro, wanda ya jefa dubban mutane cikin yanayi na gudun hjjira a sassa daban-daban na kasahse masu tasowa ciki har da Najeriya.

Wani dan jarida mai suna Sani Ibnu Salifu y ace taro irin wannan na kara tunatar da ‘yan jarida cewa da bukatar ya tabbatar bai yi wamfani da aikinsa wajen sawa a cutar da wani dana dam kamarsa ba. Ita ma Malama Odinga Odiou ta ce an sake tunatar da su cewa bai kamata su goyi bayan wani bangare ba tsakanin makiyaya da manoma.

Ga wakiliyarmu Zainab Babaji da cikakken rahoton:

Your browser doesn’t support HTML5

Rikicin Manoma Da Makiyaya: An Hori ‘Yan Jarida Kan Rahotonin Kawo Salama