Barkewar rikicin kabilanci tsakanin kabilun Hema da Lendu a arewa maso gabashin Jamhuriyar Dimokradiyar Konko ya rutsa da mutane fiye da 24 lamarin da rundunar samar da zaman lafiya ta MDD ta ce zata bincika
WASHINGTON DC —
Barkewar wani rikicin kabilanci a Arewa maso gabashin Jamhuriyar Demokaradiyyar Congo, ya yi sanadiyyar hallaka mutane sama da 24, da kuma kona daruruwan gidaje kurmus.
Jami’an kasar Congo, sun bayyana cewa rikicin ya barke ne a satin da ya gabata a lardin Ituri tsakanin ‘yan kabilar Hema da ‘yan kabilar Lendu.
Babu tabbacin abinda ya haifar da rikicin, amma an san cewa kungiyoyin biyu sun dade suna gaba mai tsanani da junansu.
Rundunar samar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya, MDD, a Kongo din, ta ce zata yi binciki akan lamarin.