Rikicin Kabilanci A Jihar Plateau

Motar Jami'an Yan Sanda.

Rundunar Tsaro ta Special Task Force (STF) a jihar Plateau, ta cafke mutane 8 da take zargi da hannu wajen rikici tsakanin kabilar Berom da Irigwe a karamar hukumar Bassa dake jihar.

Kakakin rundunar ta STF a jihar Plateau kaftin Ike, ya shaidawa wakiliyar Muryar Amurka Zainab Babaji cewa tun kwanaki Uku da suka gabata suka sami labarin tashin hankali a kauyen Camama inda suke kokarin shawo kan lamarin.

Shima shugaban matasan kabilar Berom na kasa, Coji Ciwan, yace tun ranar Litinin ake ta kokarin neman hanyar da za a kwantar da hankalin matasa, amma abin na dada lalacewa.

A cewar shugaban kungiyar raya al’ummar Irigwe, fadan dai ya fara ne tun watan 11 na shekarar da ta gabata, an kuma kashe mutane bakwai tare a kona gidajen mutane dayawa.

Sabon rikicin dai ya faru ne yayin da al’umma ke ganin zaman lafiya ya dawo a jihar Plateau.

Domin karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Rikicin Kabilanci A Jihar Plateau - 3'50"