Al’ummar jihar Nasarawa sun bayyana fargabar gudanar da sahihin zabe a shekara ta 2015, ganin yadda ake ta tashe-tashen hankali a wasu garuruwa abinda yayi sanadin rushe garuruwan da suka zama tamkar kufai yanzu haka kuma jama’a na gudun hijira zuwa wasu garuruwa da-ban-da-ban.
Rikicin na jihar Nasawa da ya ki ci ya ki cinye wa, ya fi kamari ne tsakanin kabilun Eggon, Alago Fulani da da sauransu. Abinda wasu ke gani rikin na iya shafar zabe mai zuwa kasancewar yadda mutane da dama suka guje ma mahallan su.
Sakataren Myatti Allah na jihar Nasarawa Alhaji Mohammed Hussaini, ya fadi cewa yanzu dai bata gari ne ke fakewa suna haddasa rikici a garin, kuma a ganinsa wannan ba zai shafi zabe ba in har gwamnati ta dauki mataki.
A ‘yan kwanakin nan, a ziyar da kwamitin da Speta-Janar din ‘yan sanda Najeriya ke yi don samo hanyoyin sasanta matsalolin tashin hankali a Najeriya. Da ya isa jihar ta Nasarawa ya bayyana takaicin sa bisaga irin barnar da ya gani.
Shugaban kwamitin, mataimakin Speta-Janar Christopher Dega, ya bayyana ma manema labarai cewa akwai dubban jama’a dake gudun hijira daga jihar a makwabtan jihojin plateau, da Benue, da Taraba dake cikin matsanancin wahalar rayuwa kuma suna neman agajin gaggawa.
Your browser doesn’t support HTML5