Rikicin IPMAN Na Ta Ta’azzara

  • Ibrahim Garba

Yadda karancin mai ke haddasa rudu a Najeriya

Rikicin kungiyar gamayyar dillalun man fetur a Najeriya na neman wanzuwa da kuma kawo cikas ga tafiye-tafiye da kuma wadatar man a arewa maso gabas

Rikicin shugabancin Hadakar Kungiyar Dillalan Man Fetur A Najeriya IPMAN na demar wanzuwa zuwa Jahohi da kuma shafar harkokin sufuri da kuma raba mai a shiyyar Yola, wadda ta kunshi Adamawa da Taraba.

A shiyyar ta Yola, akwai bangarori biyu – bangaren Alhaji Abubakar Butu da ta Alhaji Dahiru Buba Kaburuye, ta yadda har sai da hukumar kungiyar ta kasa ta shiga tsakani. Shugaban kungiyar a shiyyar Arewa maso gabas, Alhaji Aminu Adamu, bayan wani taron sirrin da su ka yin a kungiyar a Yola, ya kira manema labarai, inda ya nemi da a kai zuciya nesa.

Shi kuwa Alhaji Abubakar Butu, y ace za su yi kokarin ganin cewa duk da halin da ake ciki, ba a samu matsala wajen raba mai a shiyyar ba. Shi ma Alhaji Baba Kano Aliyu Jada, daya daga cikin shugabannin kungiyoyin a matakin kasa, y ace matsalar ta samo asali ne tun sama da shekara guda kuma sun a kokarin shawo kanta.

Your browser doesn’t support HTML5

Rikicin IPMAN Na Kara Ta'azzara - 2' 11''