A karshen makon jiya ne rikici ya kara munana, bayan da gwamnatin Kano ta baiwa sarkin na Kano wa'adin sa'o'i 48 ya sanar da ita matsayar sa game da aikin shugabancin majalisar sarakunan jihar da gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya nadashi a kwanakin baya.
Ganin yadda lamura suka rincabe, zauren dattawan Arewa ya samar da kwamitin shiga tsakani bisa jagorancin Farfesa Ango Abdullahi wadda har ma ya gana da masu ruwa da tsaki a litinin din nan, da suka hada da dattawa a Kano, musamman masu rike da sarautu, Malamai da kuma wakilan kungiyoyin fararen hula.
Sai dai gabanin haka, dama kwamitin Janar Abdussalami Abubakar na ci gaba da nasa aikin a asirce da nufin warware wannan takaddama ta sarki da gwamnan Kano, inda harma rahotanni suka ambata cewa, wakilan kwamitin sun gana da gwamna da sarkin a Abuja babban birnin tarayyar Najeriya.
Hakan dai na faruwa ne, bayan kwanaki kalilan da gwamnatin jihar Kano tace, wasu kungiyoyin fararen hula 35 suka rubuta mata wasika , ta muradin warware rawanin Sarki Muhammdu Sanusi na biyu, bisa abin da suka kira rashin mutunta ka'idodin tafiyar da ayyukan mulkin sarautar gargajiya.
To Amma kasa da sa'o'i 24 , sai inuwar gamayyar kungiyoyin fararen hula ta Kano ta fito ta nesanta kanta da waccan wasika, al’amrarin da ya sanya masu kula da lamura ke ganin ka iya tauye kimar kungiyoyin.
Ga rahoton Mahmud Ibrahim Kwari a kan batun:
Your browser doesn’t support HTML5