Fadan da ake yi a Burkina Faso ya tsananta a cikin watanni 6 da suka gabata, abinda ya tada hankalin kasashen duniya. kungiyoyin ‘yan bindiga daban-daban na kara kai hare-hare, da yin kashe-kashe, da kuma satar jama’a.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce karuwar rikice-rikice, wasun su da bambance-bambancen addini da kabilanci suka haddasa, sun tilastawa mutane sama da dubu dari biyu da talatin da bakwai guduwa daga gidajen su. Rashin tsaro a kasar da kuma kaurar jama’a mai yawa, a cewar majalisar sun sa an rufe cibiyoyin kiwon lafiya da yawa da kuma dubban makarantu, lamarin da ya dakilewa yara kusan dubu dari uku da talatin hanyar samun ilimi.
Bugu da kari, dubban jama’a na fuskantar matsanancin karancin abinci. Mai magana da yawun hukumar ta WFP, Harve Verhoosel, ya fadawa Muryar Amurka cewa yunwa na karuwa musamman tsakanin watannin Yuni da Satunba a lokacin da abincin da aka adana ya yi kasa sosai, kafin wata kakar.