Hatsaniyar yayi sanadiyar mutuwar wani soja daya yayin da mutane 8 suka sami raunuka inda kuma 3 daga cikinsu ke cikin matsanancin hali.
Ministan ya yiwa Sojojin jawabi yana cewa abinda ya faru abin dakaici ne bai kamata ba abinda bai taka kara ya karya ba ya jawo mummunar tashin hakalin irin wanda ya faru a Dosso ba.
Daga bisani Ministan ya ziyarci wandanda suka jirkata ya kuma ziyarci ofishin ‘yan Sanda na Dosso da barikin Soja dake Dosso, domin saduwa da wadanda suka sami raunuka da yi masu fatar alher.
Ministan ya gargadi jami’an tsaron da sun tabbatar cewa irin haka bai sake faruwa ba, yana mai cewa basu da izinin yin abinda ya faru yace amma wannan zai zama darasi domin kara karfafa dangantaka tsakanin jami’an tsaro.
Manyan jami’an Sojoji da na ‘Yan Sanda dama jami’an gwamnati ne suka mara masa baya a ziyarar tashi zuwa Dosso.
Your browser doesn’t support HTML5