Rahotanni sun tabbatar da barkewar sabon rikicin tsakanin manoma da makiya inda wasu ganao ke cewa an kashe fiye da mutane takwas tsakanin bangarorin biyu.
SP Usman Abubakar kakakin rundunar 'yansandan jihar Adamawa yace an kara tura wasu jami'an 'yansanda domin maido da doka da oda a yankin.
Yace abun da ya faru mutane suna gona sai aka farmasu har wasu uku nan take suka ji rauni daga bisani daya daga cikinsu ya mutu. Yace yanzu hankulan mutane su soma kwantawa kuma ya roki jama'a kada su dauki doka a hannunsu. Kada a kai ramuwar gayya, a hada kai da jami'an tsaro.
Wannan lamarin ya faru ne yayinda kwamitin da aka kafa na lalubo bakin zaren warware rikice-rikice da ake yawan samu tsakanin makiyaya da manoma ke shirin gabatar da taron fadakarwa da fahimtar juna.
Mr. Joseph Habila wani manomi da aka yiwa barna yace abun takaici ne ma yadda a wasu lokutan makiyaya ke barin shanunsu a hannun yara kanana. Yace sun sha fada kada a dinga ba yara kiwo. Yace yara ne suke barin shanu suna cinye gonakai kamar yadda suka yiwa tashi gonar. Yace duk da haka bai taba cewa uffan ba domin yana son zaman lafiya.
Mataimakin sarkin noman jihar Adamawa Alhaji Saidu Haladu ya yi karin haske game da abubuwan dake faruwa. Yace suna shiga tsakani ne domin a warware matsalar da ake samu tsakanin manoma da makiyaya musamman yadda ake yin barna a gonaki. Yace sun zauna sun yi yarjejeniya tsakaninsu.
Alhaji Ado Badi daya daga cikin shugabannin makiyayan yace a matsayinsa na shugaba ya bukaci bangarorin biyu da a kai zuciya nesa. Yace dole ne su tabbatar da gaskiya da adalci. Mutanen da suke zuwa daga waje su yi barna dole a nemi manyansu.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5