Wani sabon rikici ya barke a janhuriyar Niger sakamakon zargin da wasu manoma sukayi na cewa makiyaya sun barnatar masu da amfanin gona.
An kwashe sa’o’I 7 ana wannan rikicin, wanda ya kai ga hasarar rayukan mutane 10, yanzu haka dai wasu mutum bakwai sun sami munanan raunuka.
Tashin hankalin ya faru ne a jiha mafi karfi dake da makiyaya da manoma a fadin kasar Niger. Irin wadannan rigingimun na maida hannun agogo baya wajen tattaunawar fahimta da akeyi tsakanin shugabannan makiyaya da manoma a kasar.
A makon jiya ma wata rigima ta balle a garuruwan Afalla, Barmu da Takananmad tsakanin makiyaya da manoma, inda manoma suka far ma makiyaya sakamakon tura dabbobinsu da sukayi cikin gonakinsu. Amma ba a sami hasarar rayuka ba.
Duk dai da kokarin da mahukumta ke yi a wannan fanni, yanzu haka dai ana cigaba da samun rashin jituwa tsakanin manoma da makiyaya wadanda sune suka fi yawa a cikin al’ummomin kasar Niger.
Your browser doesn’t support HTML5