A jamhuriyar Nijar hukumomi sun hana wasu kungiyoyi gudanar da wata zanga-zanga, lamarin da ya haifar da mummunan rikici.
Rigakafin cutar Coronavirus ne hukumomin Yamai suka bayyana a matsayin hujjar hana wa kungiyoyin CCAC gudanar da gangamin wacce zasu yi da nufin tilasta wa gwamnatin Nijar ta gurfanar da wadanda bincike ya gano cewa sun yi awon gaba da wasu makudan kudade a ma’aikatar tsaron kasar.
Shi ne mafarin jibge jami’an tsaro a wurin da aka so a yi wannan gangami.
Hukumomin kasar dai sun cafke wasu daga cikin masu fafutukan, sakamakon barkewar tarzoma a manyan titunan Yamai, inda aka samu tashin gobara bayan da hayaki mai sa hawaye ya mamaye wani shago da ke kewayen wata kasuwa, lamarin da ya haddasa mutuwar mutum 3.
Mamayar da jami’an tsaro suka yi wa dandalin Place De La Concertation ta sa matasa suka fantsama kan manyan tituna, inda aka shafe sa’o’i kusan 2 ana rikici tsakanin jami’an tsaro da matasan.
Lamarin da ya janyo tashin gobara a kasuwar Tagabati, inji wani wanda ke wurin da lamarin ya faru mai suna Mahamadou.
Sakamakon wannan tarzoma, ‘yan sandan farin kaya sun cafke mutane da dama, cikinsu har da Nouhou Arzika na jam’iyyar MPCR da Moussa Tchangari na jam’iyyar AEC da Mounkaila halidou na kungiyar Synaceb kamar yadda wani abokin tafiyarsu Diori Ibrahim ya bayyana wa wakilinmu Souley Moumini Barma.
Wani mai ra’ayin gwamnati Abdoul Moumouni Gousman ya bayyana matakin hana zanga-zangar a matsayin wata hanyar kare jama’a daga annobar da ta addabi duniya.
A yayin da Ministan cikin gida Bazoum Mohamed ya ziyarci wannan kasuwa, ya tabbatar da mutuwar mutum 3, sai dai ya ce har yanzu ba a tantance shin ko gobarar na da nasaba da wannan zanga-zanga ba ko akasin haka.
Ga cikakken rahoton a sauti.
Your browser doesn’t support HTML5