Yayinda annobar cutar sankarau ke ci gaba da halaka ‘yan Najeriya bisa dukkan alamu ana ci gaba da fuskantar matsalar karancin allurar rigakafin.
Wani matsalar karancin allurar rigakafin cutar a Abuja ya dauki wani sabon salo inda wasu Asibitoci masu zaman kansu suka fara saida allurar ga masu bukata musamman ‘yan Boko.
Wani magidanci a Abuja, da ya bukaci a sakaya sunansa yace tunda aka samu barkewar annobar suke a firgice kuma duk kokarin da suke yin a zuwa asibitoci domin yiwa ‘ya’yansu allurar rigakafi ko ace jami’an sun tashi ko kuma ace allurar ta kare.
Wakilin muryar Amurka Hassan Maina Kaina wsanda ya bi sahun lamarin yace yanzu Asibitoci masu zaman kansu suna yin allurar ana biyansu kudi Naira dubu shida da dari biyar (6,500) kowane mutun daya.
Dr.Nasiru Sani Gwarzo, Darakta a ma’aikatar lafiya ta Najeriya, yace gwamnati bata baiwa asibitoci masu zaman kansu izinin bada allurar rigakafi ba, ya kara da cewa allurar rigakafin da ake badawa itace wace gwamnnati ta tanada ta kuma tsuke yanayin yadda ake aikinta saboda gudun kada a samu ta boge ko kuma wacce ba a kula da lafiyar ta ba har ta kai muhalli.
Ya kara dacewa saboda dole a tabbatar da cewa rigakafin ta wanzu a cikin yanayi mai sanyi (cold chain) kafin a ba mutane shi yasa gwamnati ta tsare sai wuraren da aka bada izini a bada wannan rigakafi, kuma batun biyan kudi ba a yarda a biya kudi kafin a yiwa mutane rigakafi ba.
Your browser doesn’t support HTML5